Young Sheikh ya kai wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ziyara a gidan yari da ke garin Kano, inda ake tsare da shi tun bayan da kotu ta yanke masa hukunci kan wasu kalaman da ake ganin sun saba wa koyarwar addini.
Ziyarar ta jawo hankalin jama’a, inda da dama ke ganin hakan wata alama ce ta nuna kulawa, fahimta ko kuma yunkurin sasanci tsakanin bangarorin da suka sha bamban ra’ayi.
Sheikh Abduljabbar ya shahara da fahintar addini da wasu ke kallon ta a matsayin sabanin ra’ayin mafi yawan malamai, lamarin da ya janyo muhawara da ce-ce-ku-ce a fadin ƙasa.
Har yanzu ba a fitar da cikakken bayani kan musabbabin wannan ziyara ba, amma ana kallon ta a matsayin wani mataki mai nauyi a tsakanin malaman addini da al’umma gaba ɗaya.
0 Comments