About

 Dove News Hausa wata kafar yada labarai ce mai zaman kanta da ke ba da sahihan rahotanni da shirye-shirye cikin harshen Hausa. Mun himmatu wajen isar da ingantattun bayanai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da duniya baki ɗaya — tun daga siyasa, tattalin arziki, lafiya, wasanni, addini, ilimi, har zuwa al’adu da tarihi.


Manufarmu ita ce ganin al’umma ta waye kai da kai ta hanyar samun sahihan bayanai cikin sauki da harshen da ta fi fahimta. Dove News Hausa na kuma ƙarfafa matasa ta hanyar shirye-shiryen ilimantarwa, tambayoyi da kyaututtuka, da kuma ba su dama wajen koya aikin jarida ta hanyar Volunteer Media Training.


Muna amfani da hanyoyin zamani wajen yada labarai kamar blog, WhatsApp, TikTok, Facebook da YouTube, domin kaiwa da saukaka wa masu karatu da masu sauraro.


Dove News Hausa — Gidan Labarai Mai Cike da Gaskiya, Ilimi da Fadakarwa.



Post a Comment

0 Comments