Rahoton da Bankin Duniya ya fitar a watan Afrilu na shekarar 2025 ya nuna cewa Najeriya na gaba wajen yawan mutanen da ke fama da matsanancin talauci a duniya, musamman a nahiyar Afrika ta Kudu da ke gabar hamadar Sahara. Wannan rahoto ya biyo bayan nazari ne kan halin tattalin arziki da rayuwar al’umma a yankunan da suka fi fama da matsin rayuwa.
A cewar rahoton, yankin Kudu da hamadar Sahara na Afrika ya ci gaba da zama wurin da mafi yawan matalauta ke rayuwa. Sai dai abin damuwa shi ne yadda Najeriya ta haura sauran kasashen yankin wajen adadin mutanen da ke rayuwa cikin talauci mai tsanani. Bisa kididdigar da aka fitar, kusan kashi 19 cikin dari na matalautan da ke wannan yanki na Afrika suna zaune ne a Najeriya. Wannan ya sa Najeriya ta zarta kasashen da aka dade ana kallon su a matsayin cibiyoyin talauci kamar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (14%), Habasha (9%) da kuma Sudan (6%).
Wani bangare na rahoton ya nuna cewa, daga cikin kimanin mutane miliyan 695 da ake kyautata hasashen suna rayuwa cikin talauci a duniya a shekarar 2024, kusan kashi 80% suna zaune ne a yankin saharar Afrika. Wannan adadi ya yi nisa idan aka kwatanta da wasu yankunan duniya kamar Kudancin Asiya (8%), Gabashin Asiya da yankin Pacific (2%), Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika (5%), da kuma Latin Amurka da Caribbean da ke da kashi 3 cikin dari.
Binciken ya bayyana cewa duk da yawan albarkatun da Najeriya ke da su – irinsu mai, filayen noma da dimbin matasa masu aiki – kasar ta kasa amfani da su wajen rage radadin talauci da bunkasa tattalin arziki. A maimakon haka, matsaloli kamar cin hanci, rashin ingantaccen tsari, da rashin aiwatar da manufofi yadda ya kamata, sun kara jefa al’umma cikin kunci da rashin samun saukin rayuwa.
Rahoton ya kuma jaddada cewa rashin adalci wajen rabon arziki, da yawaitar zaman banza, na daga cikin abubuwan da ke kara haifar da hauhawar yawan matalauta. Wannan matsala tana bukatar gaggawar daukar matakan da za su tabbatar da habakar tattalin arziki da samar da damammaki ga kowa da kowa.
Ko da yake ana fatan gyara ta hanyar aiwatar da manufofi na rage talauci da bunkasa rayuwar al’umma, rahoton ya nuna cewa har yanzu akwai doguwar hanya kafin a kai ga canji mai ma’ana, musamman idan ba a dakile matsalolin da suka dabaibaye tsarin mulkin Najeriya ba.
0 Comments