Rundunar ƴan sanda ta jihar Jigawa ta tabbatar da cafke wani matashi ango mai suna Auwal Abdulwahab tare da abokansa uku bisa zargin su da hannu a mutuwar sabuwar amaryarsa a kauyen Tungo, cikin karamar hukumar Sule Tankarkar. Wannan al'amari ya faru ne a daren Asabar, 26 ga watan Afrilu, 2025, bayan da ake zargin angon da abokansa sun tilasta amaryar yin jima'i da karfi da yaji har ta rasa rayuwarta.
Kakakin hukumar ƴan sanda na jihar, SP Lawan Shiisu Adam, ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, bayan samun labarin aukuwar lamarin, jami'an su sun garzaya zuwa wurin da abin ya faru domin daukar matakin gaggawa. Gawar marigayiyar aka dauke zuwa Asibitin Gumel domin gudanar da binciken likita, wanda daga bisani ya tabbatar da cewa lamarin kisan ne ya yi sanadin mutuwarta. Bayan haka, an mika gawar ga iyalanta domin gudanar da jana’iza kamar yadda addini ya tanada.
An bayyana sunayen abokan da ake zargi da hannu cikin wannan aika-aika da suka hada da Nura Basiru, Muttaka Lawan, da Hamisu Musa. Rundunar ta ce an tsare su gaba ɗaya domin ci gaba da bincike, kuma suna fuskantar tuhume-tuhume masu tsanani.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar Jigawa, CP AT Abdullahi, ya bada umarnin cewa a mika shari’ar zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (SCID) dake Dutse, domin gudanar da cikakken bincike. Ana sa ran cewa bayan kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
Rahotanni sun nuna cewa wannan lamari ya tada hankalin jama'ar yankin, inda mutane da dama ke bayyana damuwarsu kan yadda rashin mutunta mata da rashin fahimta tsakanin ma'aurata ke kaiwa ga irin wadannan munanan abubuwa. Al'ummar yankin sun bukaci hukumomi da su tabbatar da adalci wajen hukunta wadanda aka samu da laifi, domin zama izina ga sauran al'umma.
Haka zalika, wasu kungiyoyin kare hakkin mata sun fara kira da a kara wayar da kai a tsakanin matasa da sabbin ma'aurata dangane da hakkin juna da yadda za a zauna lafiya a cikin aure. A cewar su, rashin ilimi game da hakkin juna da rashin kula da jin dadi tsakanin ma'aurata na daya daga cikin manyan dalilan da ke haifar da tashin hankali da mutuwar aure a wannan zamani.
Wannan kisa ya sake tabbatar da cewa har yanzu ana bukatar kara kokari wajen yaki da cin zarafin mata da kuma ilmantar da al'umma kan muhimmancin zaman lafiya, mutunta juna, da tabbatar da adalci a duk matakai na rayuwa.
Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma ana fatan hukuma za ta tabbatar da an gudanar da shari'a cikin adalci da gaskiya.
0 Comments