Yan Arewa mayuntawa ne, ku kyalesu. Nan da 2027, yunwa za ta sa su roƙi Naira dubu biyu su zabi APC

 

 

Wike Ya Ce 'Yan Arewa Surutu Kawai Suke – "Zasu Roƙi Dubu Biyu a 2027"


Kafafen sada zumunta sun karade da wasu kalamai da ake zargin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, da furta kan mutanen Arewa. Wadannan kalamai sun jawo ce-ce-ku-ce da muhawara mai zafi a tsakanin al’umma, musamman a yankin Arewa.


A cewar rahotannin da ke yawo, Wike ya bayyana cewa: “’Yan Arewa mayuntawa ne, ku kyale su, surutu kawai suke. Nan da shekarar 2027, yunwar da zata kama su da kansu zasu rika rokon a basu naira dubu biyu su zabi jam’iyyar APC.”


Wannan furuci da ake zargin Wike da shi ya girgiza mutane da dama, inda wasu ke bayyana damuwa da yadda wani babban jami’in gwamnati zai iya fadin irin wadannan kalmomi da ke da tasiri sosai kan hadin kai da zaman lafiya.


Sai dai kuma, har zuwa yanzu, Wike bai fito fili ya tabbatar da cewa ya fadi irin wannan kalami ba, haka kuma bai karyata shi ba. Wannan rashin martani daga bangarensa na kara tayar da hankali da tambayoyi daga jama’a da ‘yan jarida, suna jiran sanin gaskiyar lamarin.


Wasu na ganin cewa wannan batu wani salo ne na siyasa da ake amfani da shi wajen bata sunan wani ko jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, musamman ganin yadda zaben 2027 ke kara karatowa. A bangare guda kuma, wasu suna danganta kalaman da halayen Wike na fadin ra’ayi ba tare da boyewa ba, kamar yadda aka saba ji daga gare shi a lokuta da dama.


Har yanzu ana ci gaba da jira jin cikakken bayani daga ofishin Ministan ko ma'aikatar FCT domin samun haske game da gaskiyar lamarin.


Post a Comment

2 Comments

  1. Mayunwatane mana tunda manyan arewa suka assasa mana yunwan gangan duk da haka sai na sake zaban tinubu ba tareda ko sisiba

    ReplyDelete
  2. Wannan gaskiya ne Mr wike,mayunwatane da gaske.nan mukaga seyi tinitu ya rabamusu abinci suna Wawa,kuko 'yankudu yadingi baku kudi.tunda manyan namu sunki tausaya mana kawai kuyita yin yadda kakeso.
    AREWA YUNWA.🤪💯

    ReplyDelete