CAN Tace Sheyi Tinubu Na Da Iya Zama Shugaban Ƙasa – Bai Kamata A Batta Masa Suna A Kafafen Yada Labarai Ba




 Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihohin 19 na arewacin ƙasar da Babban Birnin Tarayya (FCT), ta nuna damuwarta kan yunkurin bata suna da ake yi wa Seyi Tinubu, ɗan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, musamman a kafafen yada labarai da na sada zumunta.


A cikin wata sanarwa da shugaban CAN na Arewa, Fasto John Joseph Hayab, ya fitar, kungiyar ta bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a daina yada labaran da ba su da tushe ko sahihanci game da Seyi Tinubu. Hayab ya bayyana cewa duk da kasancewar Seyi ɗan shugaban ƙasa ne, hakan ba yana nufin a riƙa cin zarafinsa ko bata masa suna ta hanyar jita-jita ko labaran ƙarya da ke yaduwa a kafafen sada zumunta da wasu shafukan yanar gizo.


Faston ya kara da cewa: “Saboda Seyi ɗan Tinubu ne, bai kamata a rika bata sunansa ba, da yaɗa ƙaryar da za ta iya haifar da illa ga rayuwarsa. Ya kamata mu sani cewa rayuwa za ta ci gaba bayan mulkin mahaifinsa. Idan har muna da burin gina ƙasa mai adalci da gaskiya, to dole mu daina nuna wariya da kuma yada labarai marasa tushe da suka shafi mutane kawai saboda dangantakarsu da shugabanni.”


CAN ta kuma bayyana cewa kowanne ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da dangantakarsa da shugabannin ƙasa ba, yana da damar samun ‘yancin rayuwa da kuma kariya daga cin zarafi, musamman a bainar jama’a. Kungiyar ta nanata cewa Sheyi Tinubu matashi ne da ke da damar ci gaba da taka rawar gani a harkokin shugabanci a nan gaba idan Allah ya yarda, kuma bai kamata a toshe masa hanyoyi ko a hana shi wannan damar saboda alaƙarsa da mahaifinsa.


A cewar CAN, yadda ake yaɗa labaran ƙarya da caccaka ga ‘ya’yan shugabanni ba zai haifar da da mai ido ba, illa dai ƙara rura wutar ƙiyayya da rashin gaskiya. Kungiyar ta bukaci jama’a da su daina yanke hukunci da wulakanta mutane bisa ga jita-jita ko ra’ayoyin siyasa.


Daga karshe, CAN ta shawarci kafafen yada labarai da su dinga gudanar da bincike mai kyau kafin wallafa labarai, domin gujewa yada ƙarya da ƙara tashin hankali a cikin al’umma. Hakanan, ta bukaci gwamnati da hukumomin da abin ya shafa su sanya ido wajen kare martabar kowa da kowa ba tare da nuna son zuciya ba.

Post a Comment

0 Comments