Jirgin Sojin Najeriya Ya Kashe 'Yan Sa-kai 20 a Zamfara Bisa Kuskure

 


Aƙalla mutane ashirin (20) ne suka rasa rayukansu, ciki har da ‘yan sa-kai, sakamakon harin da jirgin saman sojin Najeriya ya kai a kauyen Tungar Kara da ke karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.


Al’ummar yankin sun bayyana cewa, jirgin ya kai harin ne bisa kuskure a lokacin da 'yan sa-kai ke yunkurin kai dauki ga mutanen da ‘yan bindiga suka kai wa hari. Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun sace sama da mutane 50 da ke aikin noma, kuma a lokacin da 'yan sa-kai ke kokarin tunkarar su, sai jirgin saman sojin ya dira daga sama yana bude wuta.


Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa:


> “Mun nufi wurin da aka kai harin don ceto jama'a, sai muka hango jirgin saman soji yana sauka. Amma daga ganinmu, sai ya fara harbinmu. Wasu sun mutu, mu kuma da Allah Ya taimaka mana muka kwanta muka boye. Muna ganin kamar shima jirgin zai bugu da mu.”




Ganau sun ce ‘yan bindigar sun shigo kauyen da rana sanye da makamai a kan babura, inda suka fara harbe-harbe da kama manoma da dama. Bayan haka ne aka kira 'yan sa-kai domin su kawo dauki, amma lamarin ya rikide zuwa mummunan kuskure daga sojojin sama.


Har yanzu dai rundunar sojin Najeriya ba ta fitar da cikakken bayani kan harin ba, sai dai al’ummar yankin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ci gaba da kira da a gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar lamarin.

Post a Comment

0 Comments