Ban San Talauci Ba Sai da Na Zama Sarkin Kano" – Inji Muhammadu Sanusi II

 


Ban San Talauci Ba Sai da Na Zama Sarkin Kano" – Inji Muhammadu Sanusi II


Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa yana daga cikin manyan ‘yan Najeriya da ba su fahimci hakikanin talauci ba har sai da ya hau kujerar sarauta.


Sanusi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wani taron jama'a na musamman da aka shirya domin bikin cika shekaru 60 na tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi. A cewarsa, shugabanci nagari dole ne ya samo asali daga zuciya mai tausayawa da kishin al'umma.


Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce duk da kasancewarsa masani a fannin tattalin arziki, bai gane irin tsananin rayuwa da wahalar da talakawa ke ciki ba sai da ya hau karagar mulki a matsayin Sarkin Kano.


“Wasu daga cikin manyan ‘yan Najeriya ba su san mene ne talauci ba,” in ji shi. “Ni kaina ban fahimci matsin da jama’a ke ciki ba sai da na zama sarki. Na ga gidajen da mutane ke zaune, na ga ruwan da suke sha a kauyuka – wasu ajujuwa katanga biyu ne kacal, kuma ba su da rufi.”


Sanusi ya yi kira da a rika tafiyar da shugabanci bisa jinƙai da kyakkyawar manufa ta ceto rayuwar al’umma, yana mai cewa shugaba nagari dole ne ya fahimci halin da mabiyansa ke ciki.

Post a Comment

0 Comments