Ƙasar Saudiyya ta Amince da Sha da Siyarwar Giya a Wasu Wurare 600 A Faɗin Ƙasar

 


A cikin wani sabon mataki da ke nuna sauyin alkibla na manufofin ƙasar Saudiyya, gwamnati ta bayyana shirin bude wuraren siyar da giya har guda 600 daga nan zuwa shekarar 2026. Wannan mataki na daga cikin shirin “Vision 2030” na Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, wanda ke da nufin gyara tattalin arzikin kasar da kuma jan hankalin masu yawon bude ido da masu zuba jari daga kasashen waje.


Rahotanni daga kafafen yada labarai kamar The Guardian da The Sun sun tabbatar da cewa Saudiyya ta riga ta bude wani shagon giya a unguwar diflomasiyya ta Riyadh a farkon shekarar 2024. Wannan shine karo na farko cikin sama da shekaru 70 da aka bude irin wannan shago a ƙasar. Amma ba kowa ke da damar siyan giya ba, domin an ware wannan shago ne domin diflomasiyoyin ƙasashen waje da ba Musulmai ba.


Wannan sabon shiri na bude wurare 600 da za a rika siyar da giya, kamar yadda aka bayyana, zai kasance ne kawai a wuraren da aka keɓe, irin su manyan otal-otal masu tauraruwa biyar, wuraren shakatawa na alfarma, da kuma wuraren yawon bude ido na musamman. Wannan yana nufin cewa haramcin giya a wuraren jama’a, shaguna da gidaje zai ci gaba da kasancewa kamar yadda yake.


A cewar mahukunta, ɗaya daga cikin dalilan wannan sauyi shine yaki da kasuwar bayan fage ta giya da ake ta fama da ita a cikin ƙasar. Giya tana shiga Saudiyya ta haramtattun hanyoyi, kuma hakan yana haifar da matsaloli na lafiya da tsaro. Saboda haka, gwamnati ta yanke shawarar kafa hanya mai tsafta da za ta rage wannan matsala, tare da samun kudin shiga daga cikin harkar yawon bude ido.


Sai dai wannan mataki ya haddasa cece-kuce tsakanin al’ummar ƙasar da ma musulmi a duniya baki ɗaya. Wasu na ganin hakan tamkar take darajar dokokin addini ne, musamman ganin cewa Saudiyya ita ce cibiyar Musulunci, inda ake da Harami biyu masu alfarma – Makkah da Madinah. Amma wasu kuma na kallon sauyin a matsayin mataki na ci gaba da buɗe ƙasa ga duniya, domin habaka tattalin arziki da zamantakewa.


Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa giya mai ƙarfi wato spirits wacce ke da fiye da kashi 20% na barasa za ta ci gaba da kasancewa haramun, kuma ba za a sayar da ita a ko'ina ba. Haka kuma, za a dinga siyar da giya ne kawai ga baƙi da ba Musulmai ba.


Duk da haka, har yanzu dokar giya a Saudiyya na nan daram ga Musulmai. Musulmi da za a kama suna shan ko sayar da giya za su fuskanci hukunci mai tsanani, ciki har da dauri ko buga bulala, gwargwadon matsayi da yanayin laifin.


A ƙarshe, wannan sabon mataki ya bayyana a matsayin wani juyin juya hali a tsarin Saudiyya, inda ke kokarin daidaita al’ada da ci gaban zamani. Duk da matsin lamba daga wasu bangarori, ana sa ran cewa wannan sauyi zai taka rawar gani wajen shiryawa gasar cin kofin duniya ta 2034 da kuma taron Expo 2030 da Saudiyya za ta karɓi baƙunci.

Post a Comment

0 Comments