Wata Tsohuwa Ta Kaiwa Shugaban Ƙasar Isra'ila Hari A Birnin Isra'ila

 


Rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta bayyana kama wata tsohuwar mata da ake zargi da shirin kashe Firayim Minista Benjamin Netanyahu ta hanyar amfani da bama-bamai.


An kama matar ne kimanin makonni biyu da suka wuce tare da haɗin gwiwar hukumar leken asiri ta Shin Bet. Rahotanni sun ce matar da ke zaune a tsakiyar Isra’ila na zargin haɗa kai da wasu domin kai hari kan Firayim Ministan.


Bincike na farko ya nuna cewa ta yi niyyar amfani da na’urar fashewa wajen aiwatar da harin. Duk da an sake ta daga tsare, kotu ta hana ta kusantar hukumomin gwamnati da kuma Netanyahu.


Hukumomi sun bayyana cewa ana sa ran gurfanar da ita gaban kotu ranar Alhamis, inda za a tuhume ta da laifin haɗa baki da kuma shirin kai harin ta’addanci. Har yanzu dai ba a bayyana sunanta da kuma sahun wadanda ake zargin sun taimaka mata ba.

Post a Comment

0 Comments