Kotu Ta Yanke Wa Mawaki G-Fresh Hukunci Kan Watsa Sabbin Kuɗi a Kano

 


Wata kotu da ke yankin Tarauni, Jihar Kano, ta yanke wa mawaki Al’ameen G-Fresh hukuncin zaman gidan gyaran hali na wata biyar ko biyan tara ta naira 200,000, bayan samunsa da laifin watsa sabbin takardun kuɗi yayin wani taron nishadi.


Lamarin ya faru ne a cikin shagon Rahama Sa’idu, inda mawakin ke shagulgula da masoyansa. Hakan ya saba wa dokar CBN kan amfani da sabbin kuɗaɗe, wadda ke da nufin hana barnatar da su.


Kotu ta tabbatar da laifin bayan shigar da kara daga masu ruwa da tsaki. Wannan hukunci ya zama izina ga matasa da sauran masu nishadi a kasar.

Post a Comment

0 Comments