Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru.
Gwamnatin jihar Edo, da ke kudancin Najeriya, ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa wasu matafiya a garin Uromi, cikin ƙaramar hukumar Esan ta Arewa Maso Gabas, a ranar Alhamis. Gwamnan ya bayyana aniyarsa ta tabbatar da hukunta waɗanda ke da hannu a lamarin.
Bidiyoyi da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna kai hari kan matafiyan da suka taso daga kudancin Najeriya zuwa arewaci.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta bayyana cewa akalla mutum 16 ne suka rasa ransu, kuma yawancinsu 'yan asalin jihar Kano ne.
Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan sa-kai sun tare matafiyan, suka fitar da su daga motocinsu, suka yi musu duka, sannan suka kona su.
Wasu bayanai sun nuna cewa matafiyan na kan hanyarsu ta komawa gida domin gudanar da bukukuwan Sallah tare da iyalansu.
Sanarwar da gwamnatin jihar Edo ta fitar ta tabbatar da cewa waɗanda suka kai harin 'yan sa-kai ne.
"Binciken farko ya nuna cewa matafiya ne da suka fito daga Fatakwal, jihar Rivers, suka wuce ta yankin, inda wasu ‘yanbanga suka tare su da tunanin cewa ɓata-gari ne," in ji sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua.
Gwamnan Edo, Okpebholo, ya kai ziyara garin a ranar Juma’a, inda ya nuna alhininsa tare da tabbatar da cewa an fara bincike don gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta yi kira da a gudanar da cikakken bincike kan harin tare da hukunta masu hannu a ciki.
Shi ma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Allah-wadai da harin, yana mai kiran hukumomi da su binciki lamarin.
A yayin ziyararsa wurin da abin ya faru, Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya yaba da yadda shugabannin 'yan arewa suka kwantar da hankula da kuma yadda suka dauki matakin da ya dace domin gujewa rikici.
0 Comments