Ƙungiyar Izala Zata Maka Dan Bello A Kotu


Zargin Ɗan Bello Akan Sheikh Bala Lau: Matsayar Mu


Mun kalli bidiyon da Ɗan Bello ya wallafa, inda yake zargin Sheikh Abdullahi Bala Lau da kungiyar Izala da karɓar kuɗi daga Gwamnatin Tarayya don gina ajujuwa, sannan yana cewa an ci kuɗin ba a aiwatar da aikin ba.


Abin mamaki shi ne yadda ya kasa fahimtar takamaiman bayanan aikin da ake magana a kai. Duk wanda yake da ilimi kuma ya bincika lamarin da hankali zai fahimci gaskiyar al'amari.


Ayyukan ginin ajujuwan da Ɗan Bello ya ambata su ne Constituency Projects na Hon. Mukhtar Aliyu Betara, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Bayo/Biu/Kwaya-Kusar Federal Constituency. A cikin bayanin aikin, an bayyana cewa Hon. Betara zai gina ajujuwa ga kungiyoyin Izala da Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir ke jagoranta, da kuma wasu makarantu na Darika. Wannan aiki zai gudana ne a Kwaya-Kusar, Jihar Borno.


Sunan JOS da KADUNA da aka yi amfani da su a takardar bayanin aikin ba suna nufin wuraren ginin bane, sai dai suna bayyana rabuwar kungiyoyin Izala guda biyu ne. Wannan ya sabawa fassarar da Ɗan Bello ya yi.


Haka kuma, zargin da Ɗan Bello ya yi cewa an ware kuɗi don gina ajujuwa a JIBWIS College of Education Jega, Kebbi State shima ba daidai bane. Wannan shiri ne na Constituency Project na Sanata Muhammad Adamu Aliero, wanda shine ya aiwatar da aikin, ba kungiyar Izala ba.


Wadannan bayanai sun tabbatar da cewa Ɗan Bello bai bincika gaskiya ba kafin ya fitar da bidiyon sa.


Matsayar Mu


1. Mun kai karar sa ga Allah – Muna addu'a Allah ya bayyana gaskiya kuma ya hukunta duk wanda ke yada ƙarya.



2. Za mu maka shi a kotu – Ɗan Bello zai zo ya bada hujjoji kan bayanan da ya fitar, musamman yadda ya samo BVN, tunda ko hukuma ce zata yi irin wannan bincike, sai ta nemi izini daga mahukunta.



3. Babu wata alaƙa da wadannan zarge-zarge – Duk waɗannan bayanai da ya fitar basu da alaƙa da Sheikh Bala Lau ko ofishin sa.



4. Ɗan Bello ya san waye Sheikh Bala Lau – Kafin Sheikh Bala Lau ya zama shugaban JIBWIS, ya riga ya kasance ɗan kasuwa mai nasara, kuma yana da isassun dukiya tun kafin shugabancinsa.




Muna nan daram kan gaskiya, kuma muna da yakinin cewa karyar Ɗan Bello ba zata ci nasara ba. Insha Allah, gaskiya zata bayyana.


JIBWIS Nigeria

Post a Comment

0 Comments