A cikin wani babban ci gaba da ke janyo hankulan masana da jama’a gaba ɗaya, kasar Sin (China) ta kaddamar da asibitin farko na Artificial Intelligence (AI) a duniya, wanda aka fi sani da “Agent Hospital”. Wannan asibiti na zamani ya sanya China a sahun gaba wajen amfani da fasahar zamani domin inganta kiwon lafiya, kuma yana nuni da yadda duniya ke canzawa zuwa sabbin hanyoyi na kula da lafiya ba tare da dogaro da ɗan Adam kai tsaye ba.
Asibitin AI na kasar Sin wani babban ci gaba ne da masana daga Jami’ar Tsinghua da ke Beijing suka kirkira. Ya ƙunshi likitoci 14 da kuma jami’an jinya guda 4 – dukansu na'urorin AI ne. Abin mamaki, wadannan na’urori suna da ikon gudanar da cikakken aikin asibiti: daga ganewar cuta, gudanar da gwaje-gwaje, bayar da shawara, har zuwa kula da marasa lafiya bayan jinya. Wannan ke nuna cewa ba kawai taimakawa likitoci za su yi ba, har ma za su iya yin aikin gaba ɗaya a wasu fannoni.
A cewar rahotanni daga kafafen duniya, wannan asibiti na zamani yana da ikon kula da marasa lafiya har 10,000 a cikin ƴan kwanaki kaɗan – adadin da zai ɗauki likitocin ɗan adam sama da shekaru biyu kafin su iya kaiwa. Wannan yana nuna yanda AI ke da saurin aiki, rashin gajiya da kuma ƙwarewa wajen fitar da sakamako cikin lokaci mai ɗan gajarta.
Wani abin burgewa shi ne yadda na’urorin AI na asibitin suka ci jarrabawar MedQA da kashi 93.06% na daidaito. Wannan jarrabawa ita ce irin wadda likitoci ke rubutawa a Amurka domin samun lasisin aiki. Wannan alama ce ta yadda AI ke kara inganci da gogewa a fannin lafiya.
Sai dai duk da wannan ci gaba, akwai buƙatar kulawa da tsare-tsare na doka da ladabtarwa domin kauce wa matsalolin tsaro da tabarbarewar amincewa da fasaha. Duk wata sabuwar fasaha na bukatar a tunkare ta da hikima da shiri, musamman a fannin lafiya inda rayuwar ɗan Adam ke cikin haɗari idan aka yi kuskure.
Bugu da ƙari, masana sun ce wannan sabuwar hanya za ta taimaka matuka wajen horar da ɗaliban likitanci, domin za su iya yin gwaji da koyon aiki a cikin duniyar kama-da-gaskiya (virtual reality) ba tare da barazana ga lafiyar marasa lafiya ba.
A takaice, bude Agent Hospital a kasar Sin wani babbar alama ce ta yadda duniya ke shirin sauyawa. Idan har wannan tsarin ya yi tasiri, akwai yiwuwar sauran kasashe za su fara kwaikwaya, kuma hakan zai iya sauya dukkan tsarin kiwon lafiya na duniya baki ɗaya.
0 Comments