Ganduje Ya Amince Da Sarki Muhammad Sunusi A Matsayin Halastaccen Sarkin Kano

 


Iyalin Ganduje Sun Yi Watsi da Aminu Ado Bayero, Sun Yi Wa Sanusi II Mubaya'a a Matsayin Sarkin Kano


Jaridar The Guardian Nigeria ta ruwaito cewa, bayan dogon lokaci ana fama da rikici a harkar masarautar Kano, iyalan shugaban jam’iyyar APC na Ζ™asa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun bayyana goyon bayansu ga Khalifa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.


Rahoton ya bayyana cewa, tsohon Gwamnan Kano, Dakta Ganduje, ya amince da nadin dansa, Alhaji Jamilu Sani Umar, da aka yi a gaban fadar Sarki Sanusi a matsayin sabon Hakimin Ganduje na Ζ™aramar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.


A wani biki mai armashi da ya gudana a fadar Kofar Kudu, Sarki Sanusi ya tabbatar da nadin Alhaji Umar – dan uwan Ganduje – a matsayin Hakimin Ganduje, yayin da dimbin jama’a daga yankin suka hallara domin sabunta mubaya’arsu ga Khalifa Sanusi.


Wannan mataki na iyalan Ganduje na nuna mubaya'a ga Sanusi II na zuwa ne a daidai lokacin da jiga-jigan jam’iyyar APC ke ci gaba da nuna goyon baya ga tsohon Sarki Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kalubalantar nadin Sanusi.


Idan za a iya tunawa, iyalan Ganduje sun taka muhimmiyar rawa wajen tsige Sanusi II daga kujerar Sarautar Kano a shekarar 2020, a lokacin da Dakta Ganduje ke matsayin Gwamna.


Post a Comment

0 Comments