Hisbah Ta Kama Wata Mata Bisa Zargin Lalata Da Almajiri a Azare
Hukumar Hisbah ta kama wata mata mai sana’ar sayar da ɗan wake bisa zargin ta da aikata lalata da wani almajiri dan shekara 14 a garin Azare, da ke cikin karamar hukumar Katagum ta Jihar Bauchi.
Shugaban hukumar Hisbah na shiyyar Katagum, Malam Ridwan Muhammad Khairan, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake bayani ga manema labarai. Ya ce matar, wadda aka fi sani da suna "Baba Mai Ɗan Wake," ana zargin ta da laifin aikata fasikanci ta hanyar tilastawa da kuma yaudarar almajirin bayan ta sanya masa wani magani mai ƙarfafa sha’awa a cikin lemo.
Malam Ridwan ya ce almajirin, wanda ke yawan zuwa wajen matar domin yi mata wasu ayyukan hannu kamar wanke-wanke a Sabuwar Tashar Jama’are, ya fara hulɗa da matar ne ta wannan hanya. Daga bisani, matar ta buƙaci yaron ya riƙa kwana a gidanta, inda ta fara yaudararsa har ta kai ga yin lalata da shi fiye da sau ɗaya.
Rahoton ya ƙara da cewa, almajirin ya samu damar guduwa daga hannunta, inda ya tafi wurin mai unguwa domin neman agaji. Mai unguwar ya saurari korafin yaron, tare da bayyana damuwa kan irin halin da yaron ke ciki. Nan take suka kai rahoto ga hukumar Hisbah, wadda ta haɗu da jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) suka kama matar domin gudanar da cikakken bincike.
Bayan kama matar, an mika ta ga ofishin ‘yan sanda na sashen binciken manyan laifuka (CID) da ke Bauchi domin ci gaba da gudanar da bincike kafin a gabatar da ita gaban kotu. Hukumar ta Hisbah ta ce za a tabbatar da ganin cewa an bi duk matakan doka domin tabbatar da adalci ga yaron da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Wata majiya ta bayyana cewa wajen da Baba Mai Ɗan Wake ke gudanar da sana’arta na ɗaya daga cikin wuraren da suka zama cibiyar taruwar masu aikata laifuka a yankin. Ta ce, a lokutan da hukumomi ke gudanar da samame, ana yawan samun matasa da ’yan mata masu zaman kansu da kuma masu safarar miyagun ƙwayoyi a wajen. Wasu daga cikinsu ma kan ce suna zama ko sun saba zuwa wajen Baba Mai Ɗan Wake.
Wannan lamari ya tayar da hankulan jama’a a garin Azare, musamman ganin yadda yara kanana musamman almajirai ke fuskantar barazana a hanyoyin rayuwa da kuma rashin kulawa daga iyaye ko masu ilimantar da su. Al’ummar gari na bukatar tashi tsaye wajen bayar da gudummawa domin kare rayuwar yara da hana faruwar irin wannan mummunan lamari nan gaba.

0 Comments