An samu tashin hankali a unguwar Kan Bariki da ke cikin garin Kumo, a karamar hukumar Akko ta jihar Gombe, bayan da wata budurwa mai suna Maijidda Ilu ta kashe kanta ta hanyar fadawa cikin wata tsohuwar rijiya. Lamarin ya faru ne bisa ga cewar saurayinta, Umar, ya bayyana cewa ya daina sonta, wanda hakan ya girgiza zuciyar budurwar matuka.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa Maijidda da saurayin nata Umar sun dade suna tare a matsayin masoya. Sai dai a kwanakin baya, abubuwa suka fara sauyawa a tsakaninsu, inda aka fara samun sabani da rashin jituwa. A cewar wasu mazauna yankin, Maijidda ta shiga cikin damuwa tun lokacin da saurayin nata ya fara kaucewa daga al’amuran soyayya.
Ranar da lamarin ya faru, an ce Maijidda ta samu labarin cewa saurayin nata ya bayyana a fili cewa baya Ζ™ara sonta kuma yana shirin auren wata. Wannan bayani ya girgiza ta, inda nan take ta nuna alamun tashin hankali da damuwa.
Bayan Ι—an lokaci, sai aka wayi gari da jin cewa Maijidda ta fada cikin wata tsohuwar rijiya da ke kusa da unguwar su. Duk da Ζ™oΖ™arin ceto ta da mazauna yankin suka yi, an same ta da rai a ransa, sai dai daga bisani ta riga mu gidan gaskiya kafin a kai ta asibiti.
Lamarin ya jefa iyayen Maijidda, dangi da mazauna unguwar cikin alhini da jimami. Wata makociyarta ta bayyana cewa Maijidda yarinya ce mai halin kwarai da tarbiyya, kuma bata da matsala da kowa, sai dai kawai damuwar soyayya ta kai ta ga wannan mummunan mataki.
Hukumar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, kuma ta bayyana cewa tuni an kama saurayin nata, Umar, domin gudanar da cikakken bincike kan abinda ya faru. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ya ce za a gudanar da bincike mai zurfi domin gano ko akwai wani abu fiye da zargin da aka sani a halin yanzu.
Hukumar ta kuma bukaci matasa da su rika tuntubar iyaye ko masu basira idan suka samu wata matsala a rayuwarsu, musamman idan ta shafi soyayya ko dangantaka, domin kaucewa daukar matakin da zai iya jefa rayuwarsu cikin haΙ—ari ko barazana.
0 Comments