Gwamnatin jihar Kano tace babu Sassauci Ga Wanda ya Taɓa Addini

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kare Dokokinta na Cin Mutuncin Addini Duk da Hukuncin Kotun ECOWAS Gwamnatin Jihar Kano ta tsaya tsayin daka wajen kare dokokinta kan Masu cin mutuncin addini, duk da hukuncin Kotun ECOWAS da ke ganin wasu daga cikin dokokin sun sabawa ka’idojin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa. Kotun ta ECOWAS ta bayyana cewa wasu sassa na dokar cin mutuncin addini ba su dace da ka’idojin kare hakkin bil’adama na duniya ba, lamarin da ya jawo muhawara mai zafi a sassa daban-daban. A cikin wata sanarwa da aka rabawa Sunday PUNCH, Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa Kano ba za ta sassauta Hukuncin Ta ba, yana mai cewa jihar tana da cikakken ikon kare darajar addininta bisa tsarin mulkin kasa. Waiya ya ce: “Ba za mu bari matsin lamba daga kasashen waje ya canza mana ra’ayi ba. Nauyin da ya rataya a wuyarmu shi ne kare dabi’un al’ummarmu waɗanda suka dogara ne da addini da tarbiyya. Ko da muna girmama ra’ayoyin kasa da kasa, dokokinmu alamar zabin mutanenmu ne.” Ya kara da cewa tsarin kare wannan doka ya samo asali ne daga tsarin tarayya da Najeriya ke bi, inda kowace jiha ke da ikon kafa dokoki da suka dace da yanayin zamantakewar jama’arta, ciki har da addini da al’ada. “Ana dora mana alhakin tabbatar da zaman lafiya da kare darajar addinin mutanenmu. Wannan doka muhimmiya ce wajen cimma wannan buri, kuma za ta ci gaba da kasancewa,” in ji Waiya. Duk da amincewa da hukuncin kotun ECOWAS, Waiya ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar wajen kare tsarkin addini da tabbatar da doka da oda a jihar. “Mun amince da ikon kotun, amma dokokin da muke amfani da su dole ne su zama abin da ya dace da dabi’u da tsarin rayuwar mutanenmu,” in ji shi. Gwamnatin jihar ta nanata cewa dokokin cin mutuncin addini da take da su ba sabani bane ga tsarin doka na Najeriya, face wani bangare na tsarin dokokin kasa da ke bai wa majalisun jihohi damar yin dokoki a fannoni da dama, ciki har da na laifuka.

Post a Comment

0 Comments