
Matsayar Kungiyar Izala Kan Hukuncin Kotun ECOWAS a Kan Sashe na 210 da 382(b) na Dokar Laifuka ta Jihar Kano da Dokar Shari’ar Musulunci (2000)
Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) Nigeria, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, na bayyana matuƙar damuwa da rashin amincewa da hukuncin da Kotun ECOWAS ta yanke a ranar 9 ga Afrilu, 2025. Wannan hukunci yana buƙatar Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta soke ko ta gyara wasu sashe na dokar jihar Kano, musamman sashe na 210 da 382(b), wadanda suka shafi aiwatar da dokokin shari’ar Musulunci.
A cewar Kotun ECOWAS, wadannan dokoki sun ci karo da haƙƙin ɗan adam, kuma suna tauye 'yancin faɗar albarkacin baki. Amma a gaskiya, wannan hukunci tsoma baki ne da bai dace ba cikin ikon Najeriya na kafa da aiwatar da dokoki bisa tsarin tarayya. Har ila yau, hakan na nuni da raina tsarin addinin Musulunci wanda al’ummar jihar Kano suka runguma da hannu biyu. Jihar Kano tana da rinjayen Musulmai sama da kashi 99%, kuma tsarin shari’ar Musulunci na daya daga cikin ginshiƙan zamantakewar su.
1. Goyon bayan Kundin Tsarin Mulki:
Sashe na 38(1) na kundin tsarin mulki na Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) ya tabbatar da haƙƙin bin addini da walwalar imani. Haka kuma, Sashe na 4(7) ya baiwa majalisar dokokin jihohi ikon kafa dokoki akan laifuka da tarbiyya. Wannan ya tabbatar da cewa kafa dokar Shari’ar Musulunci da ke kunshe da sashe na 210 da 382(b) ya yi daidai da doka da tsarin mulki, musamman ganin cewa an kafa ta ne bisa bukata da amincewar al’umma.
2. Tsarkin Addini:
Sashe na 382(b) ya tanadi hukunci ga wanda ya zagi ko ya ɓata suna ga Annabi Muhammad (SAW). Wannan hukunci ya samo asali ne daga nassoshin Alƙur’ani da hadisan Annabi. A Musulunci, kare mutuncin Annabi (SAW) ba abu ne da ake sassautawa ba. Wannan laifi ba wai 'yancin faɗa bane, sai dai cin zarafin addini da tunzura jama’a, wanda ka iya haifar da rikici da ɓarna.
3. Amincewar Jama’a:
Dokar Shari’ar Musulunci ba a ɗora ta bisa zalunci ko tilas ba, an kafa ta ne bisa tsarin dimokuraɗiyya da ra’ayin al’umma. A jihar Kano, jama’a ne suka nemi dawo da wannan doka, kuma har yanzu suna goyon bayan ta. Duk wani yunƙurin soke ta ko gyara ta zai zama take haƙƙin addini da muradun jama’ar da suka zabe ta cikin kwanciyar hankali.
4. Girmama Bambanci:
A tsarin dimokuraɗiyya da ƙa’idodin haƙƙin ɗan adam na duniya, ana girmama bambancin al’adu da addinai. Hukuncin Kotun ECOWAS na iya jawo fitina da rikici tsakanin bangarorin addini, maimakon samar da zaman lafiya da fahimta.
Kammalawa:
Muna roƙon Gwamnatin Tarayya da kada ta aiwatar da wannan hukunci. Ya kamata a tsaya tsayin daka wajen kare ‘yancin Musulmai da tsarin doka da suka amince da shi. Muna kuma kira ga Musulmai da su zauna lafiya, su ci gaba da bin doka da kuma gudanar da addininsu yadda Alƙur’ani da Sunnah suka tanadar.
Sa hannu:
Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau – Shugaba
Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe – Sakatare
Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) Nigeria
0 Comments