Saudi Arabia Ta Kai Hari Kan Dakarun Houthis Na Yemen

Saudiyya Na Taimaka wa Isra’ila Tare da Hana Takunkumin Ruwan Houthi: Rikicin Yemen na Samun Sabon Salo A mako guda kacal, Saudiyya ta kai hari sau biyu a jere kan yankin Sa’ada da ke arewacin Yemen – wata cibiya mai Ζ™arfi ta mayakan Houthi. Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da Houthi ke aiwatar da takunkumin ruwa akan Isra’ila, wanda suka ayyana a matsayin martani ga kisan gilla da Isra’ila ke yi wa al’ummar Gaza. Wannan daidaituwar lokaci da tsarin hare-haren Saudiyya na sanya tambaya mai girma: Shin Saudiyya na taimaka wa Isra’ila ne kai tsaye ko a boye? Dakarun Saudiyya sun yi amfani da makamai masu linzami da gurneti wajen luguden wuta a kan al’ummar Sa’ada, abin da ke hana Houthi mai da hankali gaba Ι—aya wajen takaita zirga-zirgar jiragen ruwa da kayayyaki zuwa Isra’ila. Wannan aiki ya zo a lokacin da Houthi ke samun karbuwa a wajen wasu kasashen Larabawa da al’ummomin Musulmi saboda goyon bayan da suke nunawa al’ummar PalasΙ—inu. Tunda Houthi suka fara kakaba takunkumi a Tekun Bahar Maliya da Tekun Red Sea, Isra’ila ta shiga cikin matsanancin hali na tattalin arziki da kuma rashin isassun kayayyakin more rayuwa. Sai dai hare-haren da Saudiyya ke kaiwa yanzu ya rage karfin Houthi, lamarin da ke bai wa Isra’ila damar saukaka matsin lamba da suke ciki. Masana harkokin siyasa da diflomasiyya na ganin cewa harin Saudiyya akan Houthi a wannan lokaci na da alaka kai tsaye da burin kare Isra’ila daga takunkumin ruwa. Wasu na fassara hakan a matsayin taimako kai tsaye ga Isra’ila, musamman ganin yadda Saudiyya ba ta nuna wani yunkuri na kakkaΙ“e halayen Isra’ila a Gaza ba, duk da zaluncin da ke faruwa. Rahotanni daga Yemen sun tabbatar da cewa fararen hula da dama sun jikkata ko suka rasa rayukansu, yayin da gidaje da kasuwanni suka zama turmus. Houthi sun bayyana cewa harin Saudiyya ba zai hana su ci gaba da matsa wa Isra’ila lamba ba, amma lamarin na kara dagula yadda suke gudanar da ayyukansu a ruwa. Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil’adama na ci gaba da kira da a dakatar da hare-haren, tare da buΖ™atar kowane bangare ya daina amfani da karfin soja wajen cimma muradunsa. Sai dai har yanzu, babu wani sauyi daga Saudiyya ko Isra’ila kan wannan matsayi. Duk da cewa Saudiyya ta sha ikirarin cewa tana da matsaya tsaka-tsaki a rikicin PalasΙ—inu da Isra’ila, a aikace, hare-haren da take kaiwa akan Houthi a irin wannan lokaci na nuna cewa akwai goyon baya ga Isra’ila, ko a fili ko a bayan fage. Wannan na iya janyo fushin al’ummar Musulmi, musamman masu goyon bayan Houthi da PalasΙ—inu. Idan aka ci gaba da irin wannan salo, akwai yiyuwar rikicin Yemen ya Ι“arke da sabon salo mai haΙ—ari wanda zai iya janyo shiga tsakanin wasu Ζ™asashe da dama, tare da haifar da sabbin barazana ga tsaron yankin gaba Ι—aya.

Post a Comment

0 Comments