Kwankwaso Ba Zai Koma APC Ba – Cewar Buba Galadima

kwankwaso Ba Zai Koma APC Ba – Cewar Buba Galadima Daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP kuma na hannun daman Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, wato Buba Galadima, ya nesanta kansa da kuma jam’iyyarsa daga jita-jitar da ke yawo cewa tsohon gwamnan Kano yana shirin komawa jam’iyyar APC. A cewarsa, babu wani shiri ko tunani daga bangaren Kwankwaso ko NNPP da ke nuni da cewa za su koma jam’iyyar da suka bari. Buba Galadima ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da jaridar The Guardian, inda ya bayyana cewa Kwankwaso yana nan daram a jam’iyyar NNPP, kuma suna ci gaba da jan hankalin ’yan Najeriya zuwa ga sabuwar hanyar shugabanci da jam’iyyarsu ke fatan kawowa. Ya ce NNPP na kokarin gabatar da mafita ta siyasa ga matsalolin da ke damun kasar, ba wai kawai samun mulki ba ne a gabansu, sai dai ceto Najeriya daga halin da ta shiga. Galadima ya kara da cewa ’yan siyasar da suka gaza ne kadai ke rika tada jijiyar wuya da maganganu marasa tushe tun kafin wa’adinsu ya kare, suna kokarin karkatar da hankalin jama’a daga gazawar da ta yi musu katutu. A cewarsa, irin wannan jita-jita na dawowar Kwankwaso APC wata hanya ce da makiya ke kokarin bata hoton NNPP da jagoranta. A baya-bayan nan, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa akwai yiwuwar Kwankwaso zai dawo jam’iyyar APC. Ganduje, wanda ya taba yin mataimakin Kwankwaso a matsayin gwamnan Kano, ya ce yana da tabbacin cewa tsohon ministan tsaro zai dawo jam’iyyar da suka rabu da ita a baya. Sai dai Galadima ya mayar da martani, yana mai cewa babu wani tunani daga gare su na komawa jam’iyyar APC, musamman idan aka yi la’akari da yadda jam’iyyar ke tafiya a karkashin Ganduje. A cewarsa, Ganduje mutum ne da ya samu shugabanci ba bisa cancanta ba, illa kawai don yana da kusanci da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Ya ce da ba don goyon bayan Tinubu ba, da babu yadda za a ce Ganduje ya dace da shugabancin jam’iyya a matakin kasa. Galadima ya ci gaba da cewa, “Idan ma za mu koma APC, shin Ganduje ne zai sanar da hakan? Babu shakka, da Ganduje ne shugaba, to koda ba a faɗa ba, ba za mu koma ba. Tinubu ne kadai ya sa aka ɗora shi a wannan matsayi, amma ba zai iya sa mu mu bi APC ba.” Ya kuma kara da cewa babu wani dan siyasa mai hankali, musamman daga Kano ko wani yanki na Najeriya, da zai yi alfahari da jam’iyyar APC a karkashin jagorancin Ganduje. A cewarsa, shugabannin APC na yunkurin amfani da sunan NNPP da Kwankwaso don samun suna a kafafen yada labarai, duk da cewa NNPP na tafiya da tsarin gaskiya da adalci. A karshe, Galadima ya jaddada cewa Kwankwaso da jam’iyyarsa za su ci gaba da gina jam’iyyar NNPP a matsayin madogara ga Najeriya, tare da fatan kawo sauyi na gaskiya a tsarin mulki da shugabanci. Ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan NNPP, domin ita ce mafita ta siyasa ga al’ummar kasar.

Post a Comment

0 Comments