Hukumar Hisbah Ta Kano Ta Kama Matashi Bisa Zargin Yin Bidiyon Batsa Da Akuya Don Yin Suna a TikTok

Hukumar Hisbah Ta Kano Ta Kama Matashi Bisa Zargin Yin Bidiyon Batsa Da Akuya Don Yin Suna a TikTok Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta cafke wani matashi mai shekaru 24 da haihuwa mai suna Shamsu Yakubu, bisa zargin aikata mummunar dabi'a da wata akuya a wani bidiyo da ya yada a kafar TikTok. Rahotanni da PUNCH Metro ta samo ranar Alhamis sun bayyana cewa an kama Yakubu ne a ranar Talata, bayan ya bayyana a wani bidiyo da Ya Saka wani ya dauke shi yayin da Yake lasar al’aurar akuya. Bidiyon ya bazu a kafafen sada zumunta, musamman a TikTok, inda ya tayar da kura da fushi daga mabukata da dama. A cikin bidiyon, an ce Yakubu ya bayyana cewa manufarsa ita ce ya samu farin jini a kafafen sada zumunta. "Na yi hakan ne don in yi Suna a kafar sada zumunta, kuma in zama sananne," in ji shi. Wasu daga cikin mazauna unguwar da suka kalli bidiyon sun fusata matuka, har ma suka yi barazanar kai masa farmaki kafin wani shugaban al'umma ya shigo tsakani ya kai rahoto ga hukumar Hisbah. Duk da haka, yayin da ake yi masa tambayoyi a gaban jami’an Hisbah, Yakubu ya musanta yin lasar al’aurar akuya Da Yayi. "Inda Ya Ce Ya rantse da Allah, Bai lasa al’aurar akuyar ba. Na kai bakina ne kusa da wurin kawai. Ya kuma kara da cewa, "Ba na shan miyagun kwayoyi, kuma ni cikin hankalina nake. Wannan shine karo na farko, kuma ba zan kara ba." Da yake magana da manema labarai, Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar Hisbah, Sheikh Aminuddeen Abubakar, ya bayyana bacin ransa kan wannan mummunan lamari. "Abin takaici ne ace musulmi zai kai bakinsa wajen al’aurar akuya, ba tare da la’akari da koyarwar addini da dabi’u masu kyau ba," in ji shi. Sheikh Aminuddeen ya kuma soki jahilcin matashin kan addini da tarbiyya, yana cewa: "Shi hankalinsa yana kan neman shahara ta hanyar aikata abubuwan ban kunya a kafar sada zumunta. Saboda haka muka umurci a duba lafiyar kwakwalwarsa da yi masa gwajin miyagun kwayoyi domin a tabbatar da halin da yake ciki." Ya kuma bayyana cewa za a kai akuyar asibitin dabbobi domin gwaji. "Eh, za mu kai akuyar asibitin dabbobi domin a duba ko ta kamu da wata cuta daga gare shi. Daga nan kuma sai mu duba lafiyar sa kafin a gurfanar da shi a gaban kotu," in ji shi. A karshe, Sheikh Aminuddeen ya ja kunnen duk wanda ke da niyyar yin irin wannan danyen aiki don neman farin jini a intanet. "Duk wanda aka kama yana wanka da datti ko toka ko gawayi don neman shahara, za a kama shi kuma a dauki matakin da ya dace a kansa," ya gargadi Al'umma.

Post a Comment

0 Comments