Ƙungiyar RID Ta Kalubalanci Gwamnatin Kano Kan Dokar Batanci Da Ta Saba Da Yarjejeniyar ECOWAS

Ƙungiyar RID Ta Kalubalanci Gwamnatin Kano Kan Dokar Batanci Da Ta Saba Da Yarjejeniyar ECOWAS Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam mai zaman kanta, Rivers in the Desert (RID), ta bayyana matsanancin damuwarta dangane da yadda gwamnatin jihar Kano ke ƙin amincewa da hukuncin Kotun ECOWAS da ya bayyana dokokin batanci da jihar ke amfani da su a matsayin masu take ’yancin ɗan adam. Wannan na zuwa ne bayan hukuncin kotun ECOWAS da aka yanke a ranar 9 ga Afrilu, 2025, wanda ya ce dokokin da ake amfani da su a Kano sun sabawa tanade-tanaden ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin bil’adama. Kotun ECOWAS ta bayyana cewa Sashe na 210 na Dokar Laifuffuka da Sashe na 382(b) na Dokar Shari’a ta jihar Kano, waɗanda ke tanadar da hukuncin kisa ga wanda aka samu da laifin batanci, suna take haƙƙin faɗar albarkacin baki da kuma ’yancin addini. Hukuncin kotun ya nuna cewa irin wannan doka ba ta dace da tsarin kare haƙƙin ɗan adam ba, kuma Najeriya a matsayinta na mamba a kungiyar ECOWAS tana da nauyin gyara irin waɗannan dokoki domin su dace da ƙa’idojin kasa da kasa. Ƙungiyar RID ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Kano da su mutunta hukuncin kotun ta hanyar soke waɗannan dokoki ko aƙalla a gyara su. RID ta bayyana cewa dokar batanci tana zama barazana ga walwalar jama’a, musamman ga masu ra’ayi daban ko ’yan tsiraru da ke da bambance-bambancen akida. Kungiyar ta ce hukuncin kisa saboda faɗar albarkacin baki abu ne da ya sabawa ƙa’idojin dimokuraɗiyya da walwala. Sai dai a martaninta, gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba za ta soke dokokin batanci da ke cikin tsarin shari’arta ba. Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa dokokin suna da tushe a cikin tsarin mulkin Najeriya, kuma suna kare addini da al’adun al’ummar Musulmi na jihar. A cewarsa, “Dokokinmu sun dace da tsarin shari’ar Najeriya, kuma suna wakiltar ra’ayin al’ummar mu. Ba za mu yarda wani hukunci daga ƙasashen waje ya tilasta mana mu sauya dabi’unmu na addini da al’ada ba.” Rikicin tsakanin ka’idojin ƙasa da ƙasa da na cikin gida ya ƙara dagula lamarin, musamman a shafukan sada zumunta inda masu rajin kare haƙƙin ɗan adam ke ganin cewa gwamnati na ƙin amincewa da gaskiya da adalci. Wasu na ganin hukuncin kotun ECOWAS wata dama ce ta fara sabuwar tattaunawa kan muhimmancin daidaita dokokin addini da na dimokuraɗiyya. Har yanzu dai ba a samu wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ko ma’aikatar shari’a ta tarayya ba dangane da matakin da gwamnatin tarayya za ta ɗauka kan wannan hukunci. Sai dai ana sa ran za a ci gaba da samun martani daga ƙungiyoyi da masana shari’a kan wannan batu mai sarkakiya.

Post a Comment

0 Comments