
Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Waƙar Eedris Abdulkareem da Ta Caccaki Tinubu
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dauki matakin haramta waƙar da sanannen mawaki Eedris Abdulkareem ya saki kwanan nan, wadda aka fi sani da "Sheyi Tell Your Papa". Wannan waƙar ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta da kafafen yada labarai, sakamakon yadda take caccakar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kai tsaye da kuma yanda take bayyana matsalolin da kasar ke ciki a halin yanzu.
A cikin waƙar, Eedris Abdulkareem ya yi amfani da kalmomi masu zafi wajen sukar halin da kasar ke ciki karkashin mulkin Tinubu, yana mai bayyana cewa Sheyi – ɗan Shugaban kasa – ya kamata ya gaya wa mahaifinsa irin halin kuncin da ‘yan Najeriya ke ciki. Mawakin ya jaddada cewa ba za su ci gaba da zama shiru ba yayin da ‘yan kasa ke fama da yunwa, hauhawar farashi, da rashin tsaro.
Rahotanni daga majiyoyi masu tushe sun tabbatar da cewa hukumar tace fina-finai da waƙoƙi ta Najeriya (NFVCB) ta bukaci a goge waƙar daga duk wani dandali na yanar gizo, ciki har da YouTube da sauran shafukan yada waƙa. Haka kuma, an umarci gidajen rediyo da talabijin da su daina kunna waƙar nan take.
Wannan matakin ya haifar da mahawara mai zafi tsakanin ‘yan Najeriya. Wasu na ganin matakin ya tauye ‘yancin fadar albarkacin baki da kuma adawa da mulkin kama karya, yayin da wasu ke goyon bayan gwamnati, suna mai cewa waƙar na iya tayar da zaune tsaye ko tada hankalin jama’a.
Eedris Abdulkareem dai ba sabon masani ba ne a fagen waƙoƙin siyasa da suka kunshi sukar gwamnati. Tun kafin wannan, ya yi fice da waƙoƙi irin su "Nigeria Jaga Jaga", wacce ta shahara sosai saboda tsantsar gaskiyar da ta kunsa, duk da cewa ita ma gwamnati ta ƙi amincewa da ita a lokacin.
Yanzu haka, ana ci gaba da sa ido kan yadda al’ummar Najeriya da masu rajin kare ‘yancin faɗar albarkacin baki za su mayar da martani kan wannan haramta.
0 Comments