Kotun ECOWAS ta buƙaci a soke dokar hukunta masu ɓatanci ga Annabi (S.A.W) a Najeriya.

Kotun ECOWAS Ta Bukaci Gwamnatin Tinubu Ta Soke Dokar Hukunta Masu Yi Wa Annabi (S.A.W) ɓatanci Kotun ECOWAS ta buƙaci Gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu da ta soke duk wata doka da ke ba da damar hukunta waɗanda ake zargin sun yi ɓatanci ga Annabi Muhammad (S.A.W). A cewar kotun, irin waɗannan dokoki na ci gaba da take haƙƙin ɗan Adam kuma suna sabawa tsarin dimokuraɗiyya da ya tanadi 'yancin faɗar albarkacin baki. Wannan hukunci ya biyo bayan ƙarar da wata kungiya mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, Expression Now Human Rights Initiative, ta shigar a gaban kotun. Kungiyar ta bayyana cewa dokar ta haddasa kama mutane da dama ba tare da bin ka’ida ba, tare da tsare su na dogon lokaci, abin da ke barazana ga ‘yancin fadin albarkacin baki a ƙasar. Kotun ta bayyana cewa Najeriya na da alhakin kare ‘yancin jama’a, musamman ma fannin ra’ayi da addini, ba wai takura su da dokokin da za su iya janyo cin zarafi ko gallaza musu ba. A gefe guda, wasu 'yan Najeriya na kallon wannan hukunci da mamaki, suna cewa idan dai wannan gwamnati na da kishin musulunci, kuma lallai gwamnatin “Muslim-Muslim ticket” ce kamar yadda ake cewa, to kamata ya yi ta tashi tsaye ta kare martabar Annabi Muhammad (S.A.W) ba tare da amincewa da tsarin da suke masa kallon kafirci ba.

Post a Comment

0 Comments