
A wata babbar kotu da ke Ζ™asar Amurka, an bayar da umarni ga manyan jami’an tsaro na Ζ™asar su fitar da wasu muhimman bayanai da suka shafi binciken da aka gudanar a shekarun 1990, wanda ya shafi shugaban Najeriya na yanzu, Bola Ahmed Tinubu. Alkalin kotun, Mai shari’a Beryl Howell, ya bayyana cewa kin bayyana irin wadannan bayanai ga al’umma ba wani abu ne mai ma’ana ba, musamman idan aka yi la’akari da muhimmancin gaskiya da adalci a cikin harkokin shugabanci da tsaron kasa.
Wannan umarni ya zo ne biyo bayan wata kara da wani Ι—an Ζ™asa Ba’amurke mai suna Aaron Greenspan ya shigar a watan Yuni na shekarar 2023. Greenspan ya shigar da karar ne bisa tanadin dokar ’yancin fitar da bayanai (Freedom of Information Act – FOIA), inda ya bukaci a tilasta wa wasu hukumomin tsaron Amurka da suka hada da FBI, DEA, CIA da kuma ofishin babban lauyan gwamnati na tarayya su fitar da duk wasu bayanai da suka shafi binciken da suka taba yi kan Bola Tinubu da wani mutum mai suna Abiodun Agbele.
A cewar Greenspan, wadannan hukumomi sun karya dokar FOIA ta hanyar kin cika wa’adin da aka kayyade na fitar da bayanan. Ya ce gazawar fitar da wadannan bayanai tamkar kokari ne na boye abubuwan da jama’a ke da hakkin sani, musamman ma idan batun ya shafi wanda ke rike da madafun iko a kasar sa. Ya yi nuni da cewa bayanan da ake nema na da muhimmanci wajen fayyace tarihin shugaban da kuma tantance gaskiyar wasu rahotanni da suka dade suna yawo a kafafen yada labarai.
Mai shari’a Howell ta amince da cewa akwai bukatar a fitar da bayanan domin kara fahimtar yadda aka gudanar da binciken, da kuma tabbatar da gaskiya cikin tsarin shari’a da mulki. Ta bayyana cewa irin wannan buΖ™ata na da matukar amfani wajen tabbatar da gaskiya a cikin dimokuraΙ—iyya, tare da kare hakkin jama’a na samun bayanai daga hukumomi.
Wannan mataki na kotun na iya zama babban ci gaba wajen karfafa tsarin gaskiya da fitar da bayanai a tsakanin hukumomin Amurka da kuma a cikin tsarin gwamnati gaba Ι—aya.
0 Comments