Sharuɗɗan Da Aka Gindaya Wa Kwankwaso Idan Har Yana Son Komawa Jam’iyyar APC

YANZU-YANZU: Sharuɗɗan Da Aka Gindaya Wa Kwankwaso Idan Har Yana Son Komawa Jam’iyyar APC Rahotanni sun bayyana cewa akwai wani yunƙuri daga bangaren tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, na komawa jam’iyyar APC. Sai dai, an gindaya masa wasu sharuɗɗa guda goma kafin a amince da dawowarsa cikin jam’iyyar. Ga jerin sharuɗɗan kamar haka: 1. Gidan Kwankwasiyya: Za a sauya sunan gidan Kwankwasiyya dake titin Miller Road zuwa Gandujiyya Holy House, tare da saka babbar banner mai dauke da hoton Ganduje a kofar gidan. 2. Faɗaɗa Hotunan Gidauniyar APC: Ya buga kalanda guda 1000 da ke dauke da hotunan Abdullahi Abbas, Nasiru Gawuna da Goggo, sannan ya yada su a fadin jihar Kano. 3. Wakar Taro: Duk lokacin da zai halarci taro, sai ya yi tafiya da wakar Ganduje da Rarara ke rerawa, wato “Ganduje shugaban party.” 4. Jar Hula: Ya ci gaba da saka jar hularsa ta al’ada, amma sai an rubuta “GANDUJE FOR EVER” a jikinta. 5. Maganar Sarauta: Ya janye kansa daga duk wata magana kan sarauta, ya kuma roƙi Sanusi Lamido ya koma Lagos, ya bar wa Alhaji Aminu Ado Bayero mulkin Kano. 6. Takara a 2027: Ya tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf ba zai sake tsayawa takarar gwamna ba, har sai Barau Maliya ya yi mulki sau biyu a jere. 7. Takara ta Shugaban Ƙasa: Ya yi alƙawarin ba zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba har sai Bola Tinubu ya kammala wa’adin sa, Shettima ya yi nasa guda takwas, sannan Ganduje ya yi takwas – sai ya zo. 8. Rabon Kujeru: Kujeru a matakin jiharsu za a raba su bisa tsarin “uku daga bangarensu, biyu daga ɓangaren Ganduje,” ciki har da na mataimakin gwamna da sakataren gwamnati. 9. Sauya Lakabi: Zai daina kiran kansa da Madugu ko Jagora, a koma kiran sa da sunan da malaminsa ya ba shi tun farko – Rabi’u kawai. 10. Zabe na 2027: Zai zama wakilin zabe (agent) a akwatin zabe da Ganduje zai kada ƙuri’a a Dawakin Tofa, idan Allah ya kai mu zaben 2027. Idan ya cika waɗannan sharuɗɗa, a shirye ake a gafarta masa dukkan kurakuransa na siyasa tare da masa wankan tsarki domin sabuwar farawa.

Post a Comment

0 Comments