Tinubu Ya fara Yunkurin Sauke Ganduje daga shugabancin APC domin gurbin sa da Tanko Makura

Rikici Ya Kunno Kai Tsakanin Shugaba Tinubu da Ganduje – Alamu Na Nuna Canjin Jagorancin APC Wani sabo rikici na siyasa na kunno kai a cikin jam’iyyar APC, inda rahotanni suka nuna cewa shugaban Ζ™asa Bola Ahmed Tinubu yana duba yiwuwar sauya shugabancin jam’iyyar na Ζ™asa daga hannun Abdullahi Ganduje zuwa Tanko Al-Makura. Wata majiya mai kusanci da fadar shugaban Ζ™asa ta bayyana cewa an fara duba yiwuwar maye gurbin Ganduje da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura – wanda ke da dangantaka ta kusa da tsohon shugaban Ζ™asa, Muhammadu Buhari. Rahotanni da aka samu daga jaridu sun nuna cewa, wannan mataki na cikin Ζ™oΖ™arin da fadar shugaban Ζ™asa ke yi na hana ficewar wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, musamman ‘yan asalin CPC, zuwa jam’iyyar SDP gabanin zaben 2027. Ana zargin cewa an fara tattaunawa da Al-Makura kan yi masa tayin kujerar shugaban jam’iyyar na Ζ™asa, domin samun goyon bayan Buhari da kuma janyo magoya bayansa su ci gaba da kasancewa a APC. Bisa cewar majiyoyi, ana sa ran Al-Makura zai yi jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, inda zai bayyana matsayin sa game da cigaba da kasancewa a jam’iyyar mai mulki tare da nuna goyon bayan Buhari. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu fitattun ‘yan siyasa da suka hada da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Aminu Tambuwal da Achike Udenwa ke ci gaba da kulla sabbin dabarun siyasa gabanin 2027, sakamakon rashin gamsuwa da tafiyar gwamnatin yanzu. Wani rahoto da aka samu ya nuna cewa jam’iyyar APC na fuskantar matsaloli na cikin gida, lamarin da ke sanya tambaya kan makomar jam’iyyar da kuma karfinta a zabukan da ke tafe.

Post a Comment

0 Comments