Mahukunta a Abuja Sun Markade Babura 601 da Aka Kama Suna Aiki Ba Bisa Ƙa’ida Ba
Hukumar Gudanarwa ta Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta ci gaba da ɗaukar mataki kan masu karya doka, inda ta markade babura har 601 da aka kama suna aiki ba bisa ƙa’ida ba a cikin Abuja.
Wannan mataki yana daga cikin jerin matakan da hukumar ke ɗauka domin hana zirga-zirgar babura a cikin babban birnin, wanda aka haramta tun shekarar 2006. A cewar Daraktan Hukumar Kula da Harkokin Hanya ta FCT (DRTS), Abdulateef Bello, tuni an markade jimillar 1,509 daga watan Agusta zuwa Disamba na shekarar 2023.
Baburan da aka kama sun fito ne daga wurare irin su Airport Road, Gudu, Lokogoma, da Games Village. Hukumar ta ce wannan aiki zai zama izina ga masu sauran niyyar karya dokokin titin birnin.
Kwamishinan ‘yan sanda na FCT, Haruna Garba, ya bayyana cewa ana amfani da babura wajen aikata laifuka da dama kamar su satar wayoyi, jakunkuna, da safarar miyagun ƙwayoyi, wanda hakan ke barazana ga tsaro.
FCTA na nanata cewa hana amfani da babura a Abuja ba kawai doka ba ce, har ila yau mataki ne na kare rayuka da dukiyoyi.
0 Comments