Isra’ila na fuskantar wata mummunar gobarar daji da ta bazu da ƙarfi a kusa da babban birnin Urushalima, lamarin da ya sanya hukumomin ƙasar ayyana dokar ta baci tare da umartar jama’a su tattara kayayyakinsu su bar yankunan da abin ya shafa.
Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, “wannan wuta tana da hatsari sosai har ma zata iya cinye birane da dama, ciki har da babban birnin ƙasa.” Ya kuma buƙaci kowa ya kasance cikin shiri don tserewa idan lamarin ya ƙara tsananta.
Masana sun bayyana cewa wannan gobara ce mafi muni da Isra’ila ta fuskanta a cikin shekarun baya-bayan nan. Tuni wutar ta lalata fiye da eka 5,000 na daji, tare da tilasta wa dubban jama’a sauya matsuguninsu da kuma rufe manyan hanyoyi, ciki har da hanyar da ke haɗa biranen Tel Aviv da Urushalima.
Rahotanni sun nuna cewa, yanayin iska mai ƙarfi da zafi ne ke ƙara yaduwar wutar. Iskar da ake kira Khamsin, na ɗauke da yashi da kuma zafin rana mai tsanani, abin da ke hana ‘yan kwana-kwana samun sauƙin shawo kan gobarar. Hakan ya sanya lamarin cikin matakin gaggawa sosai.
Hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa akwai alamun wasu daga cikin gobarun an kunna su ne da gangan, lamarin da ya sa aka cafke mutane 18 da ake zargi da hannu a ciki. Firayim Minista Netanyahu ya kira hakan da "ta’addanci", yana mai kira ga duniya da ta taimaka wajen dakile wannan annoba.
A kokarin magance wannan bala’i, Isra’ila ta samu agajin ƙasashen waje kamar Italiya, Sipaniya, Faransa, Ukraine, Romania, North Macedonia, da Cyprus, wadanda suka turo jiragen sama masu kashe gobara da kuma ƙwararrun jami’ai.
Wannan gobara ta faru ne a daidai lokacin da Isra’ila ke shirin gudanar da bikin ranar ‘yancin kai, lamarin da ya tilasta soke wasu muhimman taruka da aka shirya. An kuma ruwaito cewa mutane da dama sun samu rauni sakamakon shakar hayakin gobarar.
Al’ummar duniya, musamman ƙasashen da ke da ƙarfin fasaha, suna kira da a tashi tsaye don taimakawa wajen dakile wannan gobara da kuma kare muhalli a nan gaba.
Muna addu’ar samun sauƙi ga al’ummar Isra’ila da fatan wannan gobara za ta zama darasi ga duniya gaba ɗaya, don ƙara mayar da hankali kan hanyoyin kariyar muhalli da ingantaccen tsarin ɗaukar matakan gaggawa.
0 Comments