Ƙungiyar CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah, Don Magance Baɗala

 


Ƙungiyar CAN Ta Nemi Haɗin Gwiwar Shiga Ayyukan Hisbah, Don Magance Baɗala


Daga Mustapha Abubakar


Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen ƙaramar hukumar Sabon Gari da ke jihar Kaduna, ta bayyana bukatar samun cikakken haɗin gwiwa da hukumar Hisbah, domin yakar munanan dabi’u da kuma gina kyakkyawar mu’amala tsakanin mabiya addinai daban-daban.


Wannan kira ya fito ne daga bakin Fasto Nuhu Sani, Sakataren CAN na ƙaramar hukumar Sabon Gari, yayin da yake jawabi a wani taron bita na kwana ɗaya da hukumar Hisbah ta shirya a sakatariyar ƙaramar hukumar, domin ƙarfafa hadin kai da fahimtar juna tsakanin hukumomi da ƙungiyoyin addini.


Fasto Sani ya bayyana cewa, kasancewar hukumar Hisbah na aiki da manufofin addini wajen tabbatar da da’a da kuma kawar da ayyukan lalacewa a cikin al’umma, ya zama dole a bai wa Kiristoci damar taka rawa a wannan yunkuri. Ya ce wannan haɗin gwiwa zai taimaka gaya wajen samar da zaman lafiya da fahimta a tsakanin mabiya addinai, musamman ma a yankunan da suke rayuwa tare cikin haɗin kai.


“Mun san cewa a Sabon Gari akwai tarin mutane mabiya addinai daban-daban da suke rayuwa tare cikin lumana. Saboda haka, ya dace a ƙarfafa haɗin gwiwar aiki tsakanin Musulmai da Kiristoci domin tabbatar da tsaftar rayuwa da tarbiyya a cikin al’umma,” in ji Fasto Sani.


Ya ƙara da cewa, “Ayyukan baɗala da rashin da’a ba su takaita ga mabiyan addini guda ba, dukkan sassa na al’umma suna da rawar da za su taka wajen magance su. Don haka, haɗin gwiwar CAN da Hisbah zai haifar da kyakkyawan sakamako.”


A nasa jawabin, Kwamandan hukumar Hisbah na ƙaramar hukumar Sabon Gari, Awwal Abubakar Adam, ya bayyana cewa hukumar tana aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsafta a cikin al’umma. Ya ce Hisbah ta rufe rumfunan barasa sama da 150 da ke aiki ba tare da lasisi ba, tare da rusa otal-otal da wuraren zaman da ke bai wa ayyukan fasikanci mafaka.


Kwamandan ya bukaci sauran kungiyoyi da shugabanni a matakai daban-daban da su mara wa Hisbah baya domin tabbatar da nasarar yaki da dabi’un da suka saba wa kyawawan halaye da tsarin rayuwa.


Haka zalika, ya jinjinawa gwamnatin ƙaramar hukumar Sabon Gari bisa goyon baya da ta bayar, musamman wajen amincewa da dokar da ta bai wa Hisbah cikakken ikon gudanar da aikinta yadda ya kamata.


Jami’an tsaro daga sassa daban-daban da suka halarci taron sun bayyana goyon bayansu ga Hisbah. Cikin su har da SP Auwal Usman daga rundunar ’yan sanda, RCN Musa Sunusi daga hukumar FRSC, da ACM Aminu Amadu na hukumar kashe gobara ta ƙasa, waɗanda suka ce za su ci gaba da ba da haɗin kai wajen ganin an samu nasarar cika manufofin hukumar Hisbah.

Post a Comment

0 Comments