Matashi Ya Shiga Gidan Yari a Kano Bisa Zargin Yin Asiri da Budurwa

 Matashi Ya Shiga Gidan Yari a Kano Bisa Zargin Yin Asiri da Budurwa


Wata kotu a Kano ta yanke hukuncin dauri ga wani matashi mai suna Isah Usman, bisa zargin yin asiri da wata budurwa mai suna Mashkura, lamarin da ya jefa ta cikin hali na rashin jin kowa da gani sai shi kadai.


Rahotanni sun nuna cewa halayen Mashkura sun sauya kwata-kwata, inda ta daina hulΙ—a da iyayenta da abokanta, kana ta fara nuna halayyar da ba ta saba da ita ba, tun bayan fara hulΙ—a da Isah.


Iyayenta ne suka shigar da kara a kotu, suna zargin matashin da jefa ’yarsu cikin wani irin matsanancin yanayi na hankali da zuciya. Sun nemi kotu ta bi musu hakkinsu tare da kare lafiyar ’yarsu.


A bangare guda kuma, iyayen Isah sun musanta zargin, inda suka bayyana cewa Ι—ansu bai kai lokacin aure ba, don haka bai kamata ya yi irin wannan hulΙ—ar da yarinyar ba. Sun roki kotu da ta yi la’akari da hakan a cikin hukuncinta.


Alkali ya saurari bangarorin biyu kafin yanke hukuncin dauri ga Isah Usman, yana mai bayyana cewa akwai bukatar hukumomi su dauki matakin kare matasa daga fadawa cikin irin wannan hali.


Post a Comment

0 Comments