Sufetan Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya sake jaddada bukatar bin doka da oda wajen kame da tsare wadanda ake zargi da aikata laifi, yana mai jan kunnen jami'an rundunar da ke rike da mutane ba bisa ka’ida ba.
A cewar Egbetokun, dole ne jami’an ‘yan sanda su mutunta hakkin dan Adam, su kuma tabbatar da cewa ba su tsare wani da ya wuce wa’adin da doka ta tanada ba. Ya bayyana cewa, duk wani jami’in da aka samu yana tsare mutane fiye da lokacin da doka ta ba da dama, ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba, zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Sufetan ya kara da cewa, ana bukatar jami’an ‘yan sanda su dinga aiki da gaskiya da kuma bin ka’idojin aiki don tabbatar da adalci da kare hakkin al’umma. Ya bukaci rundunar ‘yan sandan da su rika gudanar da bincike cikin gaggawa, tare da tabbatar da cewa wadanda ba su da laifi ba su shafe lokaci mai tsawo a hannun ‘yan sanda ba.
Hakazalika, ya yi gargadi akan cin hanci da rashawa a rundunar, yana mai cewa ba za a lamunci jami’an da ke amfani da matsayin su wajen tauye hakkin ‘yan kasa ba. Ya bukaci ‘yan kasa da su rika bayar da hadin kai ga jami’an tsaro, amma su kuma su kasance masu sanin hakkinsu don kada a take musu hakkinsu ba bisa ka’ida ba.
A karshe, Egbetokun ya yi kira ga shugabannin rundunar a matakin jihohi da su tabbatar da bin wannan umarni, tare da daukar matakan da suka dace domin ganin an aiwatar da shi yadda ya kamata.
0 Comments