Masarautar Daura, jihar Katsina, ta naɗa fitaccen mawakin Hausa, Dauda Kahutu Rarara, matsayin “Sarkin Waƙar Ƙasar Hausa”, a wani taro na musamman da aka shirya domin girmama shi, lamarin da ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma.
A cewar rahotanni, Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ne ya yi wa Rarara wannan sarauta bisa la’akari da rawar da mawakin ya taka wajen waƙa da faɗakarwa a fagen ƙasar Hausa da kuma tarihin waƙoƙin siyasa da al’adu.
An shirya bikin nadin sarautar ne a fadar Sarkin Daura a ranar Asabar, 13 ga Disamba, 2025, inda Rarara ya gayyaci jama’a su halarci wannan muhimmin taro.
Sai dai wannan nadin sarauta ya haifar da ra’ayoyi daban-daban tsakanin jama’a. Wasu masoya mawakin sun taya shi murna, suna ganin wannan yabo ce ga gudummawar da ya bayar wajen bunƙasa waƙa da adana al’adun Hausawa.
A gefe guda kuma, wasu sun nuna rashin amincewa da nadin, suna mai cewa bai kamata a ba Rarara sarautar ba, bisa wasu dalilai na fahimta game da ayyukansa a baya.
Haka zalika, fitaccen mawakin ya riga ya samu wasu lambobin yabo a baya, ciki har da digirin girmamawa (honorary doctorate) daga wata jami’a ta ƙetare, saboda gudummawar da ya bayar a fannin waƙa da hidimar al’umma.

0 Comments