Ɓarayin Daji Sun Kai Sabon Farmaki a Katsina, Sun Sace Sama da Mutum 50 Tare da Halaka Wasu
A ci gaba da hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa a arewacin Najeriya, mazauna ƙaramar hukumar Funtua da ke jihar Katsina sun bayyana cewa sun fuskanci sabon hari daga Ɓarayin Daji, inda aka sace mutane sama da 50, ciki har da mata da ƙananan yara.
Majiyarmu ta BBC Hausa ta ruwaito cewa maharan sun afka wasu ƙauyuka da ke cikin yankin a cikin dare, inda suka yi ta harbe-harbe tare da lalata dukiyoyi kafin su yi awon gaba da jama’a. Wadanda aka sace sun hada da iyalai gaba ɗaya, ciki har da mata masu juna biyu da kuma kananan yara da ba su san hawa ko sauka ba.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kashe akalla mutane 6 yayin harin, wanda hakan ya jefa yankin cikin tsananin firgici da rudani. Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa mutane da dama sun tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu, yayin da wasu kuma ba a san inda suke ba har yanzu.
Har ila yau, wasu maharan sun sake kai hari a wani sashi na karamar hukumar Dandume da ke makwabtaka da Funtua, lamarin da ya kara dagula al'amura a yankin.
Wasu ganau sun ce harin ya fara ne tun ranar Asabar da daddare, kuma maharan ba su bar yankin ba har sai ranar Lahadi da rana, lamarin da ke nuna cewa jami’an tsaro ba su yi isasshen mataki ba a lokacin da ake bukatar taimako.
Yanzu haka, iyalan wadanda aka sace da ma wadanda suka rasa 'yan uwa na ci gaba da neman agaji da kariya daga gwamnati da hukumomin tsaro. Ana kuma ci gaba da rokon a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen wannan matsalar da ke ci gaba da tayar da hankalin al'umma.
0 Comments