Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun Ya Yi Kira Ga Shuwagabannin Kungiyar Izalah Na Kowanne Ɓangare Da Su Haƙura Da Saɓani, Su Hade Wuri Guda

 Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun Ya Yi Kira Ga Shuwagabannin Kungiyar Izalah Na Kowanne Ɓangare Da Su Haƙura Da Saɓani, Su Hade Wuri Guda


Fitaccen malamin addini kuma jagoran al’umma, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun, ya yi kira mai ƙayatarwa da cike da hikima ga dukkan shuwagabannin ƙungiyar Izalatul Bidi’a Wa Iqamatus Sunnah (IZALA) da ke sassa daban-daban na Najeriya da ma ƙasashen waje. A cewarsa, lokaci ya yi da shugabannin za su sanya ƙasa a gwiwa, su manta da banbance-banbancen da ke tsakaninsu, su dawo su hade guri guda don amfanin addini da al’umma gaba ɗaya.


Sheikh Yusuf ya bayyana wannan kira ne a cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta kamar wutar jeji, inda ya nuna damuwarsa game da yadda sabani da rashin jituwa ke ci gaba da raunana ƙudirin kafa ƙungiyar IZALA — wato tabbatar da koyarwar Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) da kuma yakar bidi'a.


Ya jaddada cewa:

“Idan har muna son ganin cigaba da nasarar da muka samu a baya, to wajibi ne mu kalli gaba, mu manta da abinda ya faru a baya, mu rungumi juna da zuciya ɗaya da nufin gina al’umma bisa tafarkin sunnah da ƙa’idojin addinin Musulunci.”


Kiran Sheikh Yusuf Sambo ya jawo cece-kuce da muhawara a dandalin sada zumunta, inda wasu daga cikin mabiya ƙungiyar ke nuna goyon baya ga wannan kira. Wasu na ganin wannan na iya zama wata hanya ta kawo ƙarshen rabuwar kai da ake fama da ita a tsakanin shuwagabannin da mabiya ƙungiyar a yankuna daban-daban.


A gefe guda kuwa, wasu na ganin cewa dole ne a zauna a yi sulhu da fahimtar juna domin kaucewa rikice-rikicen da kan biyo baya daga irin wannan rabuwar kai. Duk da haka, kiran da Sheikh Yusuf ya yi ya sake ɗaga hankali da haskaka bukatar hadin kai da zaman lafiya tsakanin bangarorin IZALA daban-daban.


Tarihin ƙungiyar IZALA ya nuna cewa ta fara da ƙuduri mai kyau da manufar gyara, da kuma yaki da bidi’a da tallata sunnah. Amma sabanin da ke faruwa tsakanin jagororinta ya jawo raguwar tasiri da kuma raunana sahihancin manufa a idanun wasu mabiya addinin musulunci.


Kira irin na Sheikh Yusuf Rigachikun na zama wata dabara mai amfani wadda za ta iya farfaɗo da ƙungiyar tare da dawo da martabarta, idan har za a saurare shi da zuciya ɗaya.



Post a Comment

0 Comments