
A wani mataki na kawo sauyi da gyara a fannin samar da wutar lantarki a Najeriya, Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware Naira biliyan 700 domin sayen na’urorin aunawa wutar lantarki (meters) ga miliyoyin ƴan Najeriya kafin ƙarshen shekarar 2025. Wannan bayani ya fito ne daga Ministan Harkokin Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu, wanda ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Abuja.
A cewar Ministan, gwamnatin ta fahimci irin wahalar da jama’a ke ciki wajen samun wadannan na’urori, wanda hakan ke janyo musu ƙarin kuɗin wuta ta hanyar amfani da tsarin ƙiyasta kuɗin wuta (estimated billing). Wannan tsarin ya janyo yawan ƙorafe-ƙorafe daga jama’a, inda ake caji sama da yadda aka yi amfani da wuta.
Adelabu ya bayyana cewa wannan shiri yana daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na kawo sauyi a bangaren lantarki, da kuma tabbatar da cewa kowane gida a Najeriya na da na’urar da ke aunawa daidai amfani da wuta. Ya ce, “Babu wata hanya mafi adalci wajen biyan kuɗin wuta fiye da mallakar na’urar aunawa wutar lantarki. Wannan zai tabbatar da cewa mutum yana biyan kuɗin da ya yi amfani da shi ne kawai.”
Ministan ya bayyana cewa kudin Naira biliyan 700 da aka ware za a yi amfani da su wajen sayen wadannan na’urori daga cikin gida da kuma ƙasashen waje. Haka kuma, za a tsara rabon su ne ta yadda yankunan da suka fi fama da rashin su za su fara amfana.
Ya kara da cewa za a fara aiwatar da wannan shiri cikin watanni masu zuwa, kuma ana sa ran kammala shi kafin ƙarshen shekara. Adelabu ya bukaci hadin kai daga kamfanonin raba wutar lantarki da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki domin ganin an cimma burin wannan shiri cikin nasara.
Wannan mataki na gwamnati ya zo ne a daidai lokacin da jama’a ke fama da tsadar rayuwa da rashin isasshiyar wutar lantarki. Masana harkar wuta sun bayyana wannan shiri a matsayin ci gaba, kuma suna ganin zai taimaka wajen dawo da amincewa tsakanin gwamnati, kamfanonin rarraba wuta, da masu amfani da ita.
A yanzu haka, ana jiran ganin yadda tsarin za a bi wajen raba wadannan na’urorin aunar wuta da kuma yadda jama’a za su amfana da su. Gwamnati ta bayyana cewa zata fitar da cikakken bayani a nan gaba domin kara fayyace shirin.
Tare da aiwatar da wannan shiri, ana sa ran rage matsalolin da ke tattare da rashin gaskiya a biyan kuɗin wuta, da kuma tabbatar da ingantaccen tsarin da zai amfani ‘yan ƙasa baki ɗaya.
1 Comments
💥Amee
ReplyDelete