Kotu Ta Yanke Wa Mawaki G-Fresh Hukunci Kan Watsa Sabbin Kuɗi a Kano
Mazauna kauyuka daban-daban na karamar hukumar Gusau da ke jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a jiya Laraba, domin neman gwamnati ta gaggauta daukar mataki kan tabarbarewar tsaro a yankinsu.  Dandazon al’umma daga kauyukan Mada, Ruwan Ɓore, Fegin Baza, Bangi, Lilo, Wonaka da Fegin Mahe sun hallara a kofar gidan gwamnati da ke Gusau, inda suka gudanar da zaman dirshan da nufin nuna damuwarsu kan yawaitar hare-hare da sace-sacen mutane da ke faruwa a yankunan su.  Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun iso a kafa, wasu a kan babura, wasu kuma cikin motoci, inda suka bukaci gwamnatin jihar da ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'a.  Wani daga cikin masu zanga-zangar, Malam Abubakar Abdullahi daga kauyen Fegin Mahe, ya bayyana cewa ya rasa ‘yan uwa da dama a cikin hare-haren da suka addabi yankin. Ya ce a matsayinsa na manomi kuma dan kasuwa, ya yi asarar kayayyaki da suka haura Naira miliyan ɗaya, ciki har da buhunan takin zamani guda 500 sakamakon wani hari da aka kai musu.  Da yake mayar da martani ga masu zanga-zangar, shugaban karamar hukumar Gusau, Hon. Abubakar Iman, ta bakin wakilinsa Aminu Wakili Mada, ya ba su tabbacin cewa gwamnati tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro na aiki tukuru don dawo da zaman lafiya a yankin. Ya ce tuni ana shirye-shiryen tura jami’an tsaro zuwa yankunan da lamarin ya fi tsanani.
Young Sheikh Ya Kai Ziyara Wajen Sheikh Abduljabbar a Gidan Yari na Kano
Wata Tsohuwa Ta Kaiwa Shugaban Ƙasar Isra'ila Hari A Birnin Isra'ila
Jirgin Sojin Najeriya Ya Kashe 'Yan Sa-kai 20 a Zamfara Bisa Kuskure
Ban San Talauci Ba Sai da Na Zama Sarkin Kano" – Inji Muhammadu Sanusi II
Ƙasar Saudiyya ta Amince da Sha da Siyarwar Giya a Wasu Wurare 600 A Faɗin Ƙasar